*********************************************
Daga cikin ikon da Allah ya bama Aljanu shine sukan iya daukar abu daga wani waje zuwa gurare masu nisa. Misali kamar abinda ya faru a fadar Annabin Allah, Sulaimanu (alaihis salam).
Lokacin da ya bukaci adauko masa Gadon sarautar Mulki na Sarauniya Bilqees. Sai wani IFREETU daga cikin Aljanu ya mike yace ma Annabi Sulaiman (as) "NI ZAN ZO MAKA DASHI KAFIN KA TASHI DAGA INDA KAKE ZAUNE DIN NAN".
Sannan azamanin Khalifancin Sayyiduna Umar bn Khattab (rta) Akwai wani Mutum wanda Aljanu suka daukeshi har Tsawon wasu shekaru yana wajensu, sai daga karshe Allah ya dawo dashi.
To muma awannan zamanin irin haka tana faruwa sosai. Ko mu anan ZAUREN FIQHU an sha kawo mana mutane irin wadanda Aljanun jikinsu suka ta'ba daukesu.
Misali akwai wata baiwar Allah, wacce take zaune agidan Mijinta agarin Potiskum Jihar Yobe. Tana zaune da yaranta, ta kwanta barci kenan sai Aljanun suka dauketa. Ta gaya mun cewa Kwanakinta goma sha hudu tare dasu. Wai suna yin wani biki ne, sun dauketa sun kaita har wasu Qasashen waje irin su Misra, Bangladesh, Pakistan da sauransu.
A sanadiyyar zamanta acikinsu har sun koya mata yaren Urdu (wani yare ne wanda aka fi magana dashi ayankin Asia). Acikin wannan Qankanin lokacin ta iya yaren, kuma har Yanzun nan tana iya magana da yaren.
Alokacin da mukayi mata Rukyah mun tarar da wani Aljani ajikinta mai suna "ILYASU" yace wai yana son zai aureta ne, shi yasa ya tafi da ita Wajen Bikinsu domin ya nunata adanginsa. (Abun mamaki).
Hakanan akwai wani bawan Allah (Mai gadi ne awata Makaranta) Wani Aljani ya daukeshi ya kaishi wata Qasa mai nisa, ya nuna masa wasu kudade masu yawa, yace masa ya dauka su tafi.. Shima yace yaga irin mutanen da suke wajen gaba dayansu babu Bakaken fata!!!
Lokacin da aka kama Aljanin da ya sacheshi din, sai yace wai ya daukeshi ne don ya nuna masa hanyar Arziki!! Yace masa zai aura masa 'Yarsa amma bai amince ba, shi yasa ya daukeshi.
Hakanan ko kwanan nan an kawo wata yarinya wacce tayi Shekaru Hudu ahannun Aljanu!! Sun dauketa suna son zasu kafirtata amma basu samu nasara ba.
Ire-iren Wadannan abubuwan suna faruwa sosai acikin al'Ummah.
Mai neman Qarin bayani ya nemi littafin AKAMUL MARJAAN na Badruddeen Abu Abdillah Ash-Shibliy (ra). Acikinsa akwai irin Wadannan labarurrukan wadanda suka faru tun daga zamanin sahabbai da tabi'ai. (wato abubuwan mamaki wadanda suka faru atsakanin Aljanu da mutane).
Ya Allah ka kiyayemu daga sharrin Mutane da Aljanu. Ameeen.
DAGA ZAUREN FIQHU (13-05-2016).


gashina na yanxu
ReplyDelete